logo

HAUSA

Nan bada jimawa ba `yan Najeriya zasu fara amfani da tsarin sadarwar Internet kyauta a wasu muhimman wurare

2023-03-30 10:28:52 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya zata kashe Naira biliyan 24.20 wajen samar da na`urorin sadarwar internet a wasu daga cikin filayen jiragen saman kasar da kasuwanni da kuma makarantu.

Gwamnatin ta amince da hakan ne a ranar laraba 29 ga wata yayin taron mako-mako na majalissar zartarwar kasar wanda aka gudanar a birnin Abuja karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A lokacin da ya ke karin haske ga manema labarai dake fadar shugaban kasa, ministan sadarwa na tarayyar Najeriya Farfesa Isah Ali Pantami ya ce samar da na`urorin  sadarwar ta internet a wadannan kebantattun wurare zai taimaka wajen kawo saukin gudanar al`amura ta fuskar inganta sha` anin hada-hadar kasuwanci da walwalar matafiya da sadarwa tsakanin tashoshin jiragen sama kana da saukaka sha`anin koyo da koyarwa a makarantu.

Farfesa Isah Ali Pantami ya ce an zabo filayen jiragen sama na cikin gida da na kasa da kasa daga shiyyoyi shidda na kasar.

Ha ila yau ministan sadarwa na tarayyar Najeriya ya ce an zabo manya cibiyoyin ilimi da kuma kasuwannin da za su ci gajiyar wannan shirin na amfani da internet cikin sauki kuma kyauta ba tare da biyan ko da sisin kwabo ba daga kowacce shiyyar kasar.

“Filayen jiragen sama 20 ne da suka hada da na kasa da kasa da kuma na cikin gida aka zabo da za su ci gajiyar tsarin, sannan kuma akwai manyan cibiyoyin ilimi 43 da aka sanya a tsarin sai kuma wasu daga cikin manyan kasuwanni da za a samarwa na`urar sadarwar internet din domin saukaka harkokin saye da sayarwa, kasancewar yanzu duniya ta juya hada-hadar cinikin haja ta Internet”

Shi dai wannan tsari na tsawon wa`adin watanni 5 kadai, hukumar sadarwa ta Najeriya ce za ta lura da aiwatar da shi kamar yadda ministan ya tabbatar.

Farfesa Isah Ali Pantami ya cigaba da cewa wannan shi ne karo na biyu cikin wannan shekara da gwamnati ta bullo da wannan tsarin internet mara iyaka kuma kyauta a wasu cibiyoyi, inda ya ce da farko an fara da jami`o’i 17 da kwalejin ilimi guda daya.

Yayin da yanzu kuma a karo na biyu gwamnati ta fadada zuwa manya makarantu 43 da suka kunshi jami’o’i da kwalejojin fasaha mallakin jahohi da tarayya da kuma filayen jiragen sama 20. (Garba Abdullahi Bagwai)