logo

HAUSA

Hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutane 5 a Nijeriya

2023-03-30 09:11:53 CMG Hausa

Mutane 5 sun mutu da safiyar jiya Talata, sanadiyyar taho-mu-gama da wasu motocin bas biyu suka yi a yankin arewacin Nijeriya.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasar a jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya shaidawa manema labarai a birnin Bauchi cewa, hatsarin da ya auku a kusa da kauyen Pashanu, dake kan hanyar Bauchi zuwa Jos, ya haifar da mummunar gobara.

A cewarsa, mutane 5 ne hatsarin ya rutsa da su, kuma dukkansu maza ne. Haka kuma, dukkansu sun kone kurmus ta yadda ba za a iya gane su ba, yana mai cewa, an mika su ga ‘yan sandan yankin karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi.

Yusuf Abdullahi ya kara da cewa, tayar daya daga cikin motocin bas din ya fita sanadiyyar gudun wuce kima, lamarin da ya kai ga kwacewar motar tare da yin taho-mu-gama da wata bas din, wadda ita ma ke gudu sosai. (Fa’iza Mustapha)