logo

HAUSA

Zuba Jari A Sin Tamkar Zabar Hanya Mai Bullewa Ce In Ji Firaministan Kasar Sin

2023-03-30 20:52:46 CMG Hausa

A yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya jagoranci zaman tattaunawa, tsakanin wakilan ‘yan kasuwar Sin da na kasashen waje, dake halartar taron Asiya na Boao na bana, wanda ke gudana a birnin Boao na lardin Hainan.

Yayin zaman, Li Qiang ya jaddada cewa, gwamnatin Sin na fatan yin aiki tare da ‘yan kasuwa, ta yadda za su karfafa kan su a wannan lokaci da duniya ke fuskantar yanayi na rashin tabbas, kana su karfafa kwarin gwiwar su, da daidaita burin da suka sanya gaba, su ci gaba da ingiza matakan ingantawa, da bunkasa ci gaba a kasar Sin, da Asiya da duniya baki daya.

Yayin zaman, wakilan ‘yan kasuwa daga Japan, da Sin, da Amurka, da Korea ta Kudu, da Birtaniya, da Italiya da sauran kasashe sun gabatar da jawabai, wadanda suka bayyana aniyar manyan kamfanonin kasa da kasa, na ci gaba da zuba jari a kasar Sin, da wanzar da ci gaba na tsawon lokaci a kasar.   (Saminu Alhassan)