logo

HAUSA

Sin Ta Yi Maraba Da Kama Aikin Dilma Rousseff

2023-03-30 20:42:53 CMG Hausa

A yau Alhamis ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin na maraba da kama aikin Dilma Rousseff, a matsayin sabuwar shugabar bankin samar da ci gaba ko NDB a takaice. Mao Ning, ta ce Sin za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da bankin NDB, za ta kuma goyawa jami’ar baya yayin da take aiki a cikin kasar.

Mao wadda ta bayyana hakan, lokacin da take amsa wata tambaya mai nasaba da batun, yayin taron manema labarai na rana-rana da aka saba gudanarwa, ta ce bankin NDB, daya ne daga manyan nasarorin da hadin gwiwar kungiyar BRICS ta haifar.

Ta ce sama da shekaru 7 da suka gabata tun bayan kafuwar sa, bankin ya samar da lamunin kudaden gudanar da ayyuka har 99, wadanda kudaden gudanar da su ya haura dalar Amurka biliyan 34, ya kuma samar da zarafin aiwatar da muhimman ababen more rayuwa, da wanzar da ci gaba a kasashe masu saurin samun bunkasuwar tattalin arziki, da kasashe masu tasowa.

Mao ta kara da cewa, baya ga mambobin da suka kirkiri bankin, karin kasashe ciki har da Bangladesh, da hadaddiyar daular Larabawa, da Masar, da Uruguay, ko dai sun zama, ko sun kusa zama mambobin bankin na NDB. Ta ce hakan na kara tabbatar da harsashi, da tasirin da hadin gwiwar BRICS ke da shi a matakin kasa da kasa.  (Saminu Alhassan)