logo

HAUSA

Guterres ya lashi takwabin hada kai da Afirka domin kawo karshen matsalar ta’addanci

2023-03-29 09:42:05 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya jaddada kudirin majalisar na hada kai da Afirka, wajen yaki da ta’addanci, yana mai gargadin cewa, ayyukan ta’addanci na kara bazuwa a sassan nahiyar.

A cewarsa, ta’addanci na kara karfi ne, ta hanyar neman da kuma amfani da rauni da rashin zaman lafiya a tsarin siyasa, da tattalin arziki da kuma tsaro.

Guterres ya shaida wa babban taron kwamitin sulhu kan yaki da ta’ddanci bukatar karfafa hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyoyin shiyya, Yana mai cewa, babu wani rukunin shekaru, ko al'ada, ko addini, ko dan kasa, ko yankin da ke da kariya daga ayyukan ta'addanci. Amma halin da ake ciki a nahiyar Afirka ya fi kowanne damuwa.

Ya ce, yanke kauna, da matsalar fatara, da yunwa, da rashin hidimomi na yau da kullum, da rashin aikin yi, da sauye-sauyen tsarin mulki na gwamnati, suna kara ci gaba da baiwa kungiyoyin 'yan ta'adda damar samun gindin zama, wanda hakan ke yin sabon tasiri kan sassan nahiyar.

A cewar Guterres, MDD na hada kai da Najeriya kan wani babban taron yaki da ta’addanci da za a yi a Afirka, kuma yana karfafa hadin gwiwa kan muhimman tsare-tsaren samar da zaman lafiya kamar babban kwamitin tsaro da ci gaba mai zaman kansa a yankin Sahel. (Ibrahim)