logo

HAUSA

Illar haramtaccen harin da Amurka ta kaiwa Iraki

2023-03-29 08:00:41 CMG Hausa

A bana ne ake cika shekaru 20, da Amurka da kawayenta suka kaddamar da yaki a kasar Iraki, ba tare da samun izini daga MMD ba, bisa hujjar cewa, ta gano makaman kare-dangi a kasar ta Iraki. Amma daga baya, an tabbatar da cewa, Iraki ba ta da irin wadannan makamai. Wannan ya kara tabbatar da zalunci da nuna fin karfi da Amurka ke nunawa kan wasu kasashe.

Wani nazarin jin ra’ayin jama’ar duniya da kafar CGTN ta gudanar, ya nuna cewa kaso 93.15 cikin 100 cikin mutanen da suka bayyana ra’ayinsu game da wannan yaki, sun nuna cewa, ya kamata Amurka ta dauki alhakin kaddamar da lyaki a Iraki.

Bayanai na nuna cewa, kaso 94.6 cikin 100 na yawan mutanen da aka ji ra’ayinsu na ganin cewa, babu wani dalilin da zai sa Amurka ta kaddamar da wannan yaki a Iraki, kuma cin zali ne  

A cikin wadannan shekaru 20, yawan fararen hula da suka mutu, ko suka jikkata, ya kai fiye da dubu 200, yayin da wasu miliyoyin mutane suka rasa gidajensu. A nasu bangare kuwa, sojojin Amurka 4,572 sun mutu, kana yawan kudin da kasar ta kashe ya kai fiye da dala triliyan 2. Abin da duniya take bukata, shi ne zaman lafiya ba yaki ba.

A gabar da aka cika shekaru 20 da kaddamar da yakin Iraki, tilas ne wasu ‘yan siyasa na Amurka su sake tunani, don dakatar da tada zaune tsaye a sauran wurare da sunan demokuradiyya, da ma tilastawa kasashe bin tsarin demokiradiyarta ba. Ya kamata kasashe su zabi tsarin demokiradiya da ma na bunkasuwa da ya dace da yanayin kasashensu. 

Hakika harin da gwamnatin Amurka da ‘yan korenta suka kaddamar a Iraki da ma sauran sassan duniya ta hanyar fakewa da sunan demokiradiya ko kare wani nau’i na muradunta, nuna fin karfi ne, don haka ya saba dokokin kasa da kasa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)