logo

HAUSA

An shirya karamin dandalin tattaunawar Boao na shekarar 2023

2023-03-29 13:36:11 CMG Hausa

A yammacin jiya Talata 28 ga wata, taron dandalin tattauna batutuwan tattalin arziki na Asiya na Boao na shekarar 2023 ya gudanar da karamin taro kan damammakin raya kasa da aka samu sakamakon shawarar “Ziri daya da hanya daya”. Mahalarta taron sun yi tattaunawa mai zurfi kan nasarori da ribar da aka samu wajen samun ci gaba da kuma boyayyun damammaki da shawarar “Ziri daya da hanya daya” ke samarwa a matsayin wata fa’ida ta al’ummar duniya ga kasashe masu ruwa da tsaki tun bayan da aka gabatar da ita shekaru goma da suka gabata.

Alkaluma sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2022, kamfanonin kasar Sin sun zuba jarin dalar Amurka biliyan 57.13 a yankunan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da aka kafa a kasashen dake shafar shawarar “Ziri daya da hanya daya”, inda suka samar da guraben aikin yi dubu 421 ga wuraren.

A cikin shekaru goma da suka gabata, an zurfafa gine-ginen yin mu’ammala bisa ga shawarar, ciki har da babban layin dogo tsakanin kasar Sin da Turai, wanda ya bude wata sabuwar hanyar zirga-zirga tsakanin Asiya da Turai, hakan ya ba da goyon baya mai karfi don tabbatar da tsarin samar da kayayyaki da na jerin sana’o’i na kasa da kasa.

Mahalarta taron sun bayyana cewa, a nan gaba, ya kamata kasashen da ke shafar shawarar “Ziri daya da hanya daya” su ci gaba da inganta hadin gwiwar cinikayya cikin 'yanci tare da abokan cinikayyarsu, ciki har da kasashen da suka hada kai wajen raya shawarar, da ci gaba da fadada tsarin yankunan ciniki cikin 'yanci masu inganci da ke shafar duniya baki daya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)