logo

HAUSA

Kasar Sin: Wajibi Ne Kasa Da Kasa Su Taimakawa Nahiyar Afrika Yakar Ta’addanci

2023-03-29 20:52:59 CMG Hausa

Wakilin kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya su taimakawa nahiyar Afrika shawo kan kalubale mafi tsanani da take fuskanta da ma barazanar ta’addanci.

Manzon musammam na kasar Sin kan harkokin Afrika, Liu Yuxi, ya shaidawa wata muhawarar manyan jami’ai ta Kwamitin Sulhu na MDD, wanda aka yi kan yaki da ta’addanci ta hanyar karfafa hadin gwiwa tsakanin MDD da hukumomin shiyya-shiyya cewa, har yanzu da sauran rina a kaba dangane da kawar da ta’addanci a Afrika.

Ya ce, kungiyoyin ta’addanci a shiyyoyin Afrika kamar BH da Lord’s Resistance Army da al-Shabab sun hada kai da kungiyoyin IS da al-Qaeda wajen tayar da hankali, inda suke cikin wani yanayi na rashin tabbas, yana mai jaddada bukatar hada kai tsakanin kasa da kasa wajen yaki da ta’addanci.

A cewarsa, ya kamata kasa da kasa su karfafa karfin Afrika na tabbatar da zaman lafiya da kanta da karfafa hadin gwiwar yaki da ta’addanci tsakanin kasashen duniya da nahiyar.

Har ila yau, ya ce kasar Sin na kira ga kasashen duniya su dauki matakai a aikace, wajen goyon bayan nahiyar a yaki da ta’addanci da samun ci gaba mai dorewa da taimakawa kasashen nahiyar fatattakar barazanar ta’addanci. (Fa’iza Mustapha)