Babu Bukatar Taron Kolin Demokuradiyya Mai Haifar Da Fada Da Juna
2023-03-29 21:49:44 CMG Hausa
An gudanar da taron kolin demokuradiyya karo na 2 a kasar Amurka daga ranar 29 zuwa 30 ga wata. Shekara guda da ta gabata ne al’ummar Amurka suka yi bikin jana'izar demokuradiyya mai salon Amurka a yayin taron karo na 1. Yanzu gwamnatin Amurka ta kau da kai daga adawar da ake nuna mata a gida da waje, ta sake yin wasan siyasa. Duniya na fuskantar sauye-sauye. Taron kolin demokuradiyya ya sake maimaita abun da ya yi a baya, Amurka ta nemi yin fito-na-fito cikin kungiyoyi da sunan demokuradiyya, tare da sake tayar da hankali a duniya. Gudanar da irin wannan taro, ya keta ruhin demokuradiyya. Ba a bukatar taron a duniya.
Ko ana tabbatar da demokuradiyya a wata kasa ko a’a, jama’ar kasar ne za su bayyana ra’ayoyinsu. Binciken ra’ayoyin jama’a da AP da cibiyar nazarin ra’ayoyin jama’a ta jami’ar Chicago suka gudanar a watan Oktoban shekarar bara ya nuna cewa, Amurkawa baligai da yawansu ya kai 9% ne kawai suke ganin cewa, ana tafiyar da harkokin demokuradiyya yadda ya kamata a Amurka. Ko da yake Amurka ba ta samu maki mai kyau a harkokin demokuradiyya ba, amma tana yunkurin shimfida demokuradiyya irin nata a kasashen ketare. A shekarun baya-bayan nan, demokuradiyya irin na Amurka ta yi ta haifar da tashin hankali da matsalar hakkin dan Adam a duniya, lamarin da ya samu adawa sosai. Kamfanin Dalia Research GmbH na kasar Jamus da kawancen kungiyoyi masu rajin tabbatar da demokuradiyya na duniya sun kaddamar da rahoto cikin hadin gwiwa da cewa, mutanen da yawansu ya kai 43% a duniya, wadanda suka yi musu tambaya, suna ganin cewa, Amurka ta kawo wa kasashensu barazana ta fuskar demokuradiyya.
Yanzu kura ba ta kwanta ba a duniya. Ana bukatar babban taron hadin kai don daidaita barazanar kasa da kasa, a maimakon taron kolin demokuradiyya mai haifar da fada da juna. Don haka Amurka ba za ta samu nasara ba wajen gudanar da taron kolin demokuradiyya. (Tasallah Yuan)