logo

HAUSA

Kasar Sin Na Adawa Da Ziyarar Jagorar Hukumomin Taiwan A Amurka

2023-03-29 20:44:34 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta nanata matsayin kasar na adawa da duk wani nau’i na dangantaka a hukumance tsakanin kasar Amurka da yankin Taiwan, tana mai jaddada cewa, ba ta amince da jagorar hukumomin Taiwan ta ziyarci Amurka ba.

Yayin taron manema labarai na yau Laraba, kakakin ma’aikatar Mao Ning, ta ce Sin ta riga ta gabatar da korafinta ga Amurka game da batun, tana mai cewa, ziyarar Tsai Ing-wen a Amurka yunkuri ne na neman goyon baya dangane da batun neman ‘yancin Taiwan.

Ta ce kasar Sin ba ta zuzuta batun, inda ta ce, Amurka tana hada kai tare da goyon bayan ‘yan awaren Taiwan, wanda ta ce abu ne mai matukar muni. (Fa’iza Mustapha)