logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sakamakon zazzabin Lassa a Najeriya ya kai 142

2023-03-29 09:25:33 CMG Hausa

Hukumomin lafiya na kananan hukumomi a Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afirka, sun bayyana cewa, daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, adadin wadanda suka mutu sakamakon zazzabin Lassa a kasar, ya karu zuwa 142.

A wani sabon bayani da cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta fitar jiya Talata ta bayyana cewa, zuwa yanzu cutar dake haddasa zazzabi mai tsanani, ta bazu zuwa jihohi 23 na kasar, inda aka tabbatar da adadin mutane 784 da suka kamu da cutar tun daga watan Janairu.

NCDC ta ce, sakamakon tsauraran matakan da gwamnati ta dauka na rage kamuwa da cututtuka, ya sa wadanda suka mutu sakamakon cutar kaiwa kashi 18.1 cikin 100, inda ta ce ya zuwa yanzu, aka tabbatar da kamuwar a kalla mutum guda a cikin kalla kashi 97 cikin 774 na kananan hukumomi 774 na kasar a bana.

A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO), kwayar cutar Lassa ce ke haddasa cutar zazzabin Lassa. Kuma galibin mutane suna kamuwa da kwayar cutar ce, ta hanyar abinci ko kayan gida da fitsari ko najasar berayen Mastomys masu dauke da kwayar cutar suka gurbata. Yawancin berayen da ke sassan yammacin Afirka na iya yada cutar. (Ibrahim)