“Taron demokuradiyya”? Ba ya nufin kome ba
2023-03-29 13:59:35 CMG Hausa
Za a kddamar da “Taron kolin demokradiyya” karo na biyu karkashin shugabancin kasar Amurka. Abin mamaki shi ne, ba sosai kafafen watsa labarai ke yada wannan batu ba. A daya daga cikin ‘yan tattaunawar da aka yi a kafafen sada zumunta na yammacin duniya, ba wai an fi mayar da hankali ne kan abubuwan da taron ya kunsa ba ne, a’a an fi mayar da hankali ne kan manufofin da aka kulla.
Abin takaici game da “Taron kolin demokradiyya” na farko da aka gudanar a Amurka a 2021 har yanzu yana nan bai gushe ba, Fiye da kasashe 20 sun kauracewa taron, mutane kadan ne suka kalli taron ta yanar gizo, kuma babu wani sakamako da aka samu a hukumance. A cikin sanarwar da ta shafi “Taron demokradiyya”, Amurka ta yi ikirarin tattauna “’yancin dan Adam”, daidaiton launin fata da sauran batutuwa. Amma, abin mamaki shi ne, da aka ga wadannan batutuwa, abu na farko da mutane ke tunani shi ne kasar Amurka, ta fi kowace kasa gazawa a wannan fanni.
A halin yanzu, tsoma bakin sojan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka da kuma yankin kudu da hamadar Sahara na karuwa. Shugaban sashen nazarin harkokin Amurka na cibiyar nazarin dangantakar kasa da kasa ta kasar Sin Wang Honggang yana ganin cewa, “Taron demokradiyya” karkashin shugabancin Amurka ba shi da wani tasiri ko kadan, wannan “Taron koli na karya” da ke da nufin haifar da rarrabuwar kawuna da adawa ba zai taba yin nasara ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)