logo

HAUSA

IGAD ta bukaci a samar da dala biliyan 2.7 domin tallafawa al’ummun da fari ke addaba a kahon Afirka

2023-03-28 09:56:27 CMG Hausa

Kungiyar bunkasa yankin gabashin Afirka ko IGAD a takaice, ta yi kira da a samar da tallafin dalar Amurka biliyan 2.69, domin ceton rayukan miliyoyin al’ummun dake fuskantar yunwa, sakamakon fari dake addabar kasashen Kenya, da Uganda, da Somaliya.

Da yake karin haske game da hakan a jiya Litinin, sakataren zartaswa na kungiyar Workneh Gebeyehu, ya ce yanayin kamfar abinci a kasashen 3 na kara ta’azzara, har ta kai mutane kimanin miliyan 47 na fuskantar rashin isasshen abinci, baya ga wadanda ke fuskantar hadarin rasa rayuka saboda yunwa.

Mr. Gebeyehu ya kara da cewa, farfadowa daga wannan yanayi na bukatar kudade da isasshen lokaci, kuma kungiyar IGAD na aiki tukuru wajen dakile mummunan tasirin wannan matsala a nan gaba.

Kungiyar IGAD ta ce fari na da mummunan tasiri ga al’ummun kasashen da lamarin ya fi shafa, inda yake haifar da kamfar ruwa, da ciyayin da dabbobi ke bukata, lamarin da tuni ya raba kimanin mutane miliyan daya da muhallan su, kana ya sabbaba mutuwar sama da dabbobin gida da na daji miliyan 10, tare da rage yawan hatsi da dabbobin da ake kiwo, matakin da ke kara ta’azzara karancin isasshen abinci da ake bukata a yankin na kahon Afirka. (Saminu Alhassan)