logo

HAUSA

Me ya sa wasu kan ji barci kullum?

2023-03-28 16:31:41 CMG Hausa

 

Masu karatu, ko kuna jin barci bai ishe ku ba duk da cewa kun dauki lokaci mai tsawo kuna barci? Kwanan baya masanan kasar Jamus sun bayyana wasu dalilai guda 8 da wasu kan ji barci ba ya isan su

Da farko, kila akwai matsala a sashen jikin dan Adam da ake kira thyroid a Turance, wanda ke samar da sinadarin Hormone don sarrafa yanayin sinadaran jikin dan Adam. Matsalar da ake fama da ita a sashen jikin dan Adam na thyroid kan sanya mutane jin barci da yawan kasala.

Na biyu, matsalar karancin sinadarin iron a jiki, musamman ma mata, kan haifar da karancin Hb cikin jini, ta yadda mutane kan ji kasala, rashin mai da hankali kan wani abu ko kuma saurin kamuwa da mura. Ta yaya za a daidaita matsalar? A kara cin nama, kayan lambu, wake da sauran abinci masu dauke da sinadarin iron da kuma bitamin C, a kokarin kara shigar da sinadarin iron a jiki.

Na uku, shan maganin yaki da cututtukan borin jini. Ya zama tilas a tabbatar da cewa, ko maganin dake sanya mutane su rika jin barci ko kuma a sha maganin da dare kafin a sha maganin.

Na hudu, rashin shan isasshen ruwa. Kullum wadanda ba sa shan isasshen ruwa, ba sa barci da kyau. Idan ba a shan ruwa da rana, to, ba za a samu isasshen barci da kyau da dare ba, kana rashin samun barci da kyau da dare, yana da nasaba da rashin shan isasshen ruwa da rana. Don haka ya fi kyau a sha ruwan da ya kai lita 1.5 zuwa 2 a ko wace rana.

Na biyar, kamuwa da ciwon sukari. Wadanda ke fama da ciwon sukari nau’in 2 kan ji gajiya da kasala.

Na shida, rashin isasshen motsa jiki. Masu karatu, ko kullum ba ku so ku motsa jiki saboda kuna gajiya? Hakika dai, wadanda ba sa motsa jiki kullum su kan ji gajiya. Don haka idan ana son yin barci da kyau, to, kamata ya yi a motsa jiki kullum.

Na bakwai, matsalar karancin bitamin B12 a jiki. Idan mutum ba shi da isasshen bitamin B12 a jikinsu, to, zai sanya shi kasa mai da hankali kan wani abu, kana fuskokinsu kan yi haske, su kan ji barci kullum. Idan ba a ci isasshen abinci ko kuma akwai karancin bitamin B12 a jikinsu, to, kila hakan zai iya haifar da matsalar karancin bitamin B12 a jiki. Don haka, Dole ne a je a ga likita.

Na takwas wato na karshe kuma, ba a sha kofi ko shayi a lokacin da ya dace. Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani cewa, idan aka sha kofi ko shayi da yamma, hakan na iya sanya mutane su kasa yin barci da dare. Don haka a rika shan kofi ko kuma shayi a lokacin da ya dace, ta yadda za a samu barci mai kyau da dare. (Tasallah Yuan)