logo

HAUSA

Yadda Amurka Take Kiyaye Hakkin Dan Adam Ya Zama Mafarki Maras Dadi

2023-03-28 21:29:52 CMG Hausa

Ranar 27 ga wata, rana ce ta matukar bakin ciki ga wasu iyalan Amurkawa. A wannan rana da safe, ‘yan shekaru tara 3 da wasu baligai 3 sun rasa rayukansu cikin harbe-harben da aka yi a makarantar firamare na birnin Nashville da ke jihar Tennessee. Mafarki maras dadi ya sake abkuwa. Ba shakka Amurka ta gamu da matsala.

Yau Talata kasar Sin ta gabatar da rahoto kan yadda Amurka ta keta hakkin dan Adam a shekarar 2022, wanda ya bayyana wa duniya gaskiyar Amurka.

Rahoton ya yi karin bayani kan yadda aka kara keta hakkin jama’ar Amurka da lalata ‘yancinsu a shekarar bara da ta gabata. Amurka ta samu koma baya wajen kiyaye hakkin dan Adam. Ban da haka kuma, rahoton ya ce, Amurka, kasa ce da ta samun harbe-harben bindiga a makarantu. A shekarar 2022 kawai, yawan harbe-harben da aka yi a makarantun Amurka ya kai 302, wanda ya kafa tarihi tun bayan shekarar 1970. Harbe-harben bindiga sun zama babban dalilin da ya haifar da mutuwar kananan yara a Amurka.

Ba a tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar Amurka ba, yayin da masu kudi suka yi amfani da kudinsu cikin zabe. Matsalar nuna bambancin launin fata ta kara yin kamari, yayin da gibin da ke tsakanin masu kudi da matalauta yake karuwa. Amurka ta gaza kiyaye hakkin dan Adam a gida. Kuma gwiwar Amurkawa ta sanyaya dangane da salon demokuradiyya da hakkin dan Adam na kasar duka. Amma kuma ‘yan siyasar Amurka sun ci gaba da sukar wa wasu kasashe.

Salon hakkin dan Adam na Amurka, mafarki ne mafi rashin dadi na Amurkawa, da ma na al’ummomin kasa da kasa. (Tasallah Yuan)