Ibrahim Bature: Ci gaban kasar Sin ya burge ni matuka!
2023-03-28 15:29:32 CMG Hausa
Ibrahim Bature, dan asalin jihar Katsina ta arewacin Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a sashin nazarin ilimin kiwon dabbobi, da magungunan dabbobi na Lanzhou na cibiyar binciken kimiyyar ayyukan gona ta kasar Sin.
A wata zantawar da ya yi da Murtala Zhang, malam Ibrahim Bature ya bayyana ci gaban kasar Sin a idanun sa, da ra’ayin sa kan muhimmancin inganta hadin-gwiwa tsakanin kasar sa wato Najeriya da kasar Sin, gami da yadda zai iya yin amfani da ilimin da ya samu a Sin wajen samar da ci gaba ga Najeriya. (Murtala Zhang)