logo

HAUSA

Za a kaddamar da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye a karon farko tsakanin Isra’ila da Najeriya

2023-03-27 10:15:33 CMG Hausa

Ma’aikatar sufurin Isra’ila, ta ce a watan Afirilun dake tafe za a kaddamar da jirgin sama na farko da zai rika zirga-zirga tsakanin kasar da tarayyar Najeriya.

Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce jirgin kamfanin “Air Peace” na Najeriya ne zai fara jigilar fasinjoji tsakanin kasashen 2, tun daga ranar 20 ga watan na Afirilu. Tuni kuma hukumomin kula da sufurin sama na kasashen biyu, suka sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta baiwa kamfanonin jiragen saman sassan 2 damar tashi da sauka, a filayen jiragen saman Ben Gurion dake wajen birnin Tel Aviv, da wasu filayen jiragen sama dake Najeriya, ciki har da na Lagos da birnin Abuja.

Cikin sanarwar, ministan ma’aikatar sufurin Isra’ila Miri Regev, ya ce Najeriya na sahun gaba a kasashen nahiyar Afirka, wadda ke kyautata alaka da kasar sa a fannoni da dama. (Saminu Alhassan)