logo

HAUSA

Rundunar sojojin Nijar FAN ta gana da daliban jami ar Abdoul Moumouni da ke Yamai da zummar kara kusanto yan kasa

2023-03-27 10:13:37 CMG Hausa

A wani kokarin kara kusanto fararen hula, rundunar sojojin kasar Nijar cewa da FAN ta fara wani jerin aikin kusanto yan kasa, wanda da ta fara da daliban jami ar Abdoul Moumouni da ke birnin Yamai, domin tattauna matsalolin tsaro da kasar Nijar take fuskanta da ma matsayin rundunar sojoji a cikin kasa mai yanci.

Daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, wakilin mu Mamane Ada, ya aiko mana da wannan rahoto.

Ganin cewa jami a, itace tushen ilimi mai nagarta, ga makomar kasa bisa cewa daga nan ne manyan gobe suke fitowa cike da kwarewa da kishin bautawa kasa, yasa shugabannin jami ar Abdoul Moumouni a karkashin jagorancin Almoustapha Bakin Batoure, da ma aikatar tsaron kasa, suka shirya zaman taron domin wata huldar dagantaka mai armashi tsakanin sojoji da fararen hula, domin fuskantar kaluben tsaro a kasar Nijar. A yayin wannan zaman taro, an tabo wasu batutuwa da ke cima yan kasa tuwo a kwarya, kamar dangantaka tsakanin sojojin Nijar da sojojin kasashen waje, anan shugabannin sojojin Nijar, sun bayyana cewa dagantaka ta shafi illa bada horo, taimakon kayayyaki da kuma samar da bayyanan soja, saidai ba za a rasa, wani lokacin ana samun halartar aikin soja tare da sojojin Faransa. In ba haka, a dukkan inda fagen daga yake to sojojin Nijar suke tafiyar da ayyukan yaki da kungiyoyin yan ta adda da tsaron kasa. Saidai, ganin cewa, Nijar nada girma da kuma matsalolin tsaro a wasu yankunan kasar, ga yawan kudaden da ake kashewa wajen yaki da ta addanci da kuma yan fashi da makamai, da masu fataucin miyagun kwayoyi, dole sai kasar Nijar ta bukacin tallafin abokan huldarta, a cewar rundunar sojojin Nijar na FAN. 

A lokacin da daliban jami ar suka aza tambayar kome me yasa sa ake samun jinkirin kai dauki ga sojojin da aka kai ma hari, anan ma sojojin sun bayyana cewa kai dauki ta sama ya nada matsala sosai domin dole sai an kaucewa kashe fararen hula, wannan nan ke sa anan samun jinkiri.

Daga karshe, shugabannin sojojin FAN da suka halarci wannan haduwa sun bada karin haske kan daukar soja, tare da bayyana cewa bisa hangen shugaban kasa Mohamed Bazoum za a kara yawan sojojin  Nijar zuwa dubu 50 nan da shekarar 2025.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.