An kammala ayyukan share fagen dandalin tattaunawar Boao na shekarar 2023
2023-03-27 14:19:08 CMG Hausa
Za a gudanar da dandalin tattaunawar Asiya na Boao na shekarar 2023 a tsakanin 28 da 31 ga watan Maris, a Boao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. A halin yanzu an riga an kammala dukkanin ayyukan share fagen taron, kuma an bude cibiyar watsa labarai a yau Litinin 27 ga wata.
Taken taron na wannan shekara shi ne "Duniyar da ba ta da tabbas: Hada kai don fuskantar kalubale, bude kofa da yin hakuri don inganta ci gaba". Kimanin baki 2,000 daga kasashe da yankuna sama da 50 ne za su halarci taron.
A yayin taron na kwanaki hudu, za a gudanar da taruka, da zaman tattaunawa, da tarukan manema labarai da yawansu ya kai kusan 50, wadanda suka kunshi batutuwa kamar shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da zamanintarwa irin na kasar Sin, da hadin gwiwar yankin Asiya, da hasashe kan tattalin arzikin duniya, da yanayin siyasa bisa bambancin sassan duniya da dai sauransu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)