logo

HAUSA

“Kungiyar Kwallon kafa na Shadi” dake kan kan hanyar neman ganin likita

2023-03-27 20:31:19 CMG Hausa

A watan Maris na shekarar 2011, an barkar da rikicin Syria. A cikin shekarun 12 da suka gabata, kasar Amurka na ci gaba da kai dauki daga dakarun soji da saka haramtattun takunkumi ta gaban kai ga Syria, lamarin da ya haddasa bala'o'in jin kai masu yawa. An tilastawa jama’ar kasar da dama tserewa daga gidajensu, kuma iyalin Hussein el Jadoua’a sun yi tattaki zuwa kasar Lebanon dake makwabtaka. Ko shakka babu zama a wata kasar waje na da wuya, ban da wannan kuma ciwon da Shadi wato dan el Jadoua’a da ya fi karami ya kamu da shi, ya kasance abun da ya fi dame dukkan iyalin nan dake shan wahalhalu. Domin tattara kudin jinya ga Shadi, ’yan uwansa maza guda uku sun fara buga kwallon kafa daya bayan daya.

Hussein el Jadoua’a da matarsa  Ourouba suna da 'ya'ya bakwai, iyalinsu sun tsere daga Idlib na Syria zuwa Lebanon don gujewa yaki, yanzu suna zaune a wani karamin gari mai suna Abbassieh dake kudancin kasar Lebanon. A nan ne sun yi hayar wani gida akan dala 80 a ko wane wata. Jadoua’a ya kan yi aiki a matsayin ma'aikaci na wucin gadi a gidajen cin abinci ko kantunan sayar da kayayyaki daban daban, amma kudin da yake samu bai isa ya biya hayar gida ba. Ban da wannan kuma, sakamakon tsadar wutar lantarki a kasar Labanon, kudaden wutar lantarkin da iyalin Jadoua’a ke biya duk wata ya haura dalar Amurka 50, wanda ko shakka babu nauyi ne mai tsanani a gare shi. Duk da haka, abin da ya fi damuwa da dukan iyalin shi ne, halin ciwo da dansa Shadi ke ciki, wato Shadi mai shekaru 13 kawai yana fama da farfadiya tun yana karamin yaro.

Ko a Siriya, inda ake fama da yake-yake, ko kuma Labanon da ke fama da matsalar tattalin arziki, rashin kula da lafiya da karancin magani matsala ce da iyalin ke fuskanta a yau da kullum. Don jinyar Shadi, mahaifiyarsa, Ourouba, ta yi iyakacin kokarinta don samun likitocin da za su yi wa Shadi magani. Domin ajiye kudi, babu dabara sai su yi tafiya da kafa. Haka kuma a kan hanyar neman ganin likita akai-akai ne, dan Ourouba na farko Mohammad ya soma mayar da hankali kan filayen kwallon kafa dake kan hanyar. Ourouba ta bayyana cewa,

“Da farko Muhammad ya yi fatan ya shiga filin wasan domin dubawa kawai. Amma, daga baya, ya yi wani kwallo da takarda da manne, ya kuma buga ta a cikin gida, gaskiya wancan kwallon kafa ne da aka yi da hannu, har ma ya taba nade kaset din a kafafunsa, kamar yana sanye da takalman kwallon kafa. A shekarar 2014, a karshe dai ya shiga filin wasa don yin wasan kwallon kafa, kuma ya dauki lambar yabo. Da na gani lambar yabon a karon farko, ban iya bayyana irin farin cikin da na yi a lokacin ba.”

Nasarorin da yaran suka samu a fannin buga kwallon kafa sun kawo farin ciki sosai ga wannan iyalin dake fama da talauci. Iyalan el Jadoua’a ya rataye duk lambobin yabo 41 da ’yan uwan hudu suka samu a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Muhammad yana da shekara 18 da haihuwa, kuma yana buga wasan kwallon kafa a matsayin dan wasan gefe na dama, ya zuwa yanzu ya riga  ya buga wasanni 320. Saboda kasancewarsa dan gudun hijira, zai iya buga wasa a matakin yanki kawai, kuma ba zai iya wakiltar kungiyoyin fasaha don yin gasar lig-lig na kasar Lebanon ba. Kanensa guda uku sun buga wasan a matsayin ‘yan wasan baya da kuma ‘yan wasan tsakiya bi da bi, ‘yan’uwan hudu sun sanyawa kansu suna “Kungiyar Kwallon kafa na Shadi”, hakan a kodayaushe suke iya tuna wa kansu ainihin burinsu na buga kwallon kafa, wato don tara kudaden jinya ga kaninsa Shadi.

Dan wasan da Muhammad ya fi sha'awar shi ne, dan wasan gaba na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, Muhammad yana da sha'awar sake maimaita labarin tsafi na tsafi na tun daga unguwar talakawa zuwa tauraron duniya a kansa, shi ma zai iya haskawa a filin wasa.

“Burina shi ne in yi suna a duniyar kwallon kafa, zan ci gaba da bin wannan hanya, zan bar sunana a duniyar kwallon kafa da kuma samu magoya baya na.”

Kasar Lebanon tana kasancewar kasar da ta fi karbar yawan ‘yan gudun hijira a duniya, an yi kiyasin cewa, a halin yanzu akwai ‘yan gudun hijirar Syria kimanin miliyan 1.5 suna zama a Lebanon, kwatankwacin kashi daya bisa uku na duk al’ummar Lebanon. Yayin da kasar Lebanon ta sha fama da matsalar kudi mafi muni a tarihin kasar, yanayin rayuwa da ‘yan gudun hijirar Syria ke ciki ma ya tabarbare matuka. ‘Yan gudun hijirar ba su ma iya biyan kudin yau da kullum, balle ma biyan kudin ilimi da kula da lafiya.

Mohammed da kannensa guda uku sun riga sun bar makaranta saboda rashin samun kudin karatu da kudin safuri, ba su da zabi sai dai su zabi buga wasan kwallon kafa, amma duk da haka kudin da suke samu wajen wasan kwallon kafa ba su iya biyan bukatun kanin sa Shadi na samun jinya. Shadi yana bukatar kulawa daga wajen iyali a dare da rana, kuma yana shan magani mafi kankanta da yake bukata don hana tsanantar halinsa. Da yake magana kan tsare-tsare na gaba, el Jadoua’a ya ce, inda makomar yaran ta kasance, zai kasance a can.

“Ba wanda ba ya son komawa garinsu, amma ba ni da komai a Siriya. Gidanmu dake Siriya, da kauyenmu, har ma duk garinmu wato Idlib sun riga sun lalace. Muna so mu bar Lebanon don zuwa wasu kasashe, yana da alaka da makomar yaranmu. Ba ni da makoma da kaina, amma yaran har yanzu suna da makomarsu, fatan su shi ne buga kwallon kafa.”