logo

HAUSA

Za a gudanar da kidayar jama’a a Najeriya

2023-03-27 10:02:13 CMG Hausa

Shugaban hukumar wayar da kan jama’a ta tarayyar Najeriya Garba Abari, ya ce za a gudanar da kidayar daukacin al’ummar kasar na shekarar 2023, tsakanin ranaikun 3 zuwa 5 ga watan Mayu, kidayar da ake fatan za ta ba da damar tantance yawan daukacin al’ummun Najeriya, da iyalai, da gine gine.

Garba Abari, wanda ya shaidawa manema labarai hakan a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce kidayar na da matukar alfanu, kasancewar za ta ba da damar tsara manufofin ciyar da kasar gaba, da tsaro, da bunkasa ababen more rayuwa, da raya ilimi da lafiya, da sauran fannoni masu nasaba da tsarin yawan al’ummu dake zaune a sassa daban daban.

Har ila yau, jami’in ya ce kidayar dake tafe, wani muhimmin aiki ne na wajibi dake gaban Najeriya, wanda zai taimaka matuka wajen tsara dabarun bunkasa kasa, da aiwatar da ayyukan ci gaba. (Saminu Alhassan)