logo

HAUSA

Sin za ta kara kyautata manufofin harkokin kudi

2023-03-27 09:49:04 CMG Hausa

Ministan ma'aikatar kudin kasar Sin Liu Kun, ya ce a bana kasar sa za ta aiwatar da karin matakai na kyautata manufar harkokin kudin ta, tare da inganta tsarin biyan haraji yadda ya kamata.

Liu Kun, wanda ya bayyana hakan yayin taron lalubo dabarun samar da ci gaba na kasar Sin na shekarar 2023 da aka bude jiya Lahadi, ya ce Sin za ta ci gaba da daukar daukacin kamfanoni da masana’antu a matsayi na bai daya, ciki har da masu zaman kan su da masu jarin waje, kana kasar za ta ci gaba da kyautata yanayin da zai ba su damar samun ci gaba.

Liu ya kara da cewa, bisa burin kasar Sin na wanzar da ci gaba mai nagarta, gwamnati za ta kara kyautata tasirin kasafin kudi, da karfafa ikon kananan hukumomi ta fuskar sarrafa takardun lamuni na musamman, don ingiza zuba jari, tare da karkata karin albarkatu ga kananan sassan gwamnati.

Kaza lika, gwamnati za ta kara inganta tsarin biyan haraji, da sauran hada-hadar biyan kudade, da kyautata cin gajiya daga salon kashe kudade, da daidaita manufofin kashe kudaden kasafin kasar tare da sauran manufofin hada-hadar kudi, da na raya masana’antu, da fasahohi, da na kyautata zamantakewar al’umma. (Saminu Alhassan)