logo

HAUSA

Kafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da Honduras ya sake tabbatar da manufar Sin daya tak a duniya

2023-03-27 10:27:08 CMG Hausa

A jiya Lahadi 26 ga wata ne, Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin da kasar Honduras suka sanar da kulla huldar diflomasiyya, bayan da Honduras ta sanar da yanke huldar jakadanci da mahukuntan Taiwan. Ya zuwa yanzu, kasashe 182 na duniya sun kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin, yayin da kasashe 13 ne kawai, hukumomin Taiwan suke kira wai “kasashe masu diplomasiyya”. Wannan ya nuna cewa, manufar Sin daya tak a duniya, ra’ayin gaba daya ne, kuma ka’idar dangantakar kasa da kasa da kasashen duniya suka amince da shi.

Kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, ita ce gwamnati daya tilo da ke wakiltar kasar Sin baki daya, kuma Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba. Wannan hujja ce ta tarihi da ta shari'a da ba za a haramta ta ba.

Bisa labari na baya bayan nan, kasar Sin tana maraba da kasar Honduras bisa yadda ta ba da goyon baya, da kuma shiga hadin gwiwar raya shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da shawarar raya kasa da kasa, da shirin samar da tsaro a duniya, da shirin wayewar kai a duniya, da sa kaimi ga yin mu’amala, da hadin gwiwa a aikace bisa tsarin da ya dace.

A sa’i daya kuma, kasar Sin tana son samar da nasarori da dama, wadanda za a iya samu cikin sauri, ta hanyar fadada shigo da kayayyaki daga kasashen waje, da karfafa zuba jari, da shiga ayyukan gina ababen more rayuwa, da ba da fifiko kan ayyukan da za su amfani rayuwar jama’a, don bayar da “riba” ga Honduras, sakamakon kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Tsayawa kan manufar Sin daya tak a duniya, adalci ne na kasa da kasa, kuma wadanda suke neman “‘Yancin Taiwan” za su yi hasara idan suka yi hannun riga da halin da ake ciki. Babu wanda ya isa ya raina kwakkwarar azama, da tsayin daka, da karfin ikon jama'ar kasar Sin na kare ikon mallakar kasa, da cikakken yankin kasa.

Dalilai za su tabbatar da karuwar kasashen da ke kasancewa a gefen dama na tarihi. (Mai fassara: Bilkisu Xin)