logo

HAUSA

Amurka ta sake zargin kasar Sin kan asalin kwayar cutar COVID-19 domin yunkurin siyasa

2023-03-26 21:22:41 CMG Hausa

A kwanakin baya, kasar Amurka ta sake zargin kasar Sin kan asalin kwayar cutar COVID-19 domin yunkurin siyasa, kuma wannan ba shi ne karo na farko da kasar Amurka ta yi hakan ba.

A kwanakin baya, hukumomin gwamnatin kasar Amurka da ‘yan siyasar kasar da kuma kafofin watsa labarun kasar, sun hada hannu kan wannan batu. Da farko, jaridar The Wall Street Journal ta tsamo rahoton sirri da ma’aikatar kula da harkokin makamashi ta kasar Amurka ta mikawa fadar shugaban kasar Amurka wato White House da majalisar dokokin kasar cewa, mai yiwuwa kwayar cutar COVID-19 ta fito daga gidan gwaji na kasar Sin ba da gangan ba. Daga baya kuma, manyan kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun ba da labarai masu ra’ayi iri daya kan wannan batu. Sai dai jakadan Amurka dake kasar Sin R. Nicholas Burns da shugaban hukumar leken asiri ta kasar Amurka wato FBI Christopher Wray, su ma sun bayyana ra’ayi kusan iri daya game da wannan batu. Amma abin ban dariya shi ne, ma’aikatar kula da harkokin makamashi ta kasar Amurka ita da kanta ta ayyana wannan rahoto a matsayin wanda ba shi da tabbaci mai karfi.

Wannan aiki ya shaida damuwar kasar Amurka kan kasar Sin. Kasar Amurka ta maida kasar Sin a matsayin babbar abokiyar gaba kan manyan tsare-tsare, inda take son matsawa kasar Sin lamba a dukkan fannoni. Zargin kasar Sin ta hanyoyi da dama, daya ne daga cikin hanyoyin Amurka na yaki da kasar Sin.

Batun neman asalin kwayar cutar COVID-19 batu ne dake shafar kimiyya da fasaha, bai kamata a yi amfani da batun domin yunkurin siyasa ba. Kasar Amurka ba za ta daidaita matsalolinta ta hanyar sake yin amfani da wannan batu ba, amma ta hakan kasa da kasa za su kara sanin cewa kasar Amurka ce ta fi kawo cikas ga aikin neman asalin kwayar cutar COVID-19 a duniya. (Zainab)