logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta ce babu wanda zai rasa aikin sa idan an bayar da hayar tasoshin jiragen sama hudu na kasar

2023-03-26 15:43:52 CMG Hausa

A ranar Alhamis 23 ga wata, ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Sanata Hadi Sirika ya tabbatar da cewa babu ma’aikacin da za a sallama ko da bayan an kammala yarjejeniyar jinginar da wasu manyan tasoshin jiragen sama hudu dake kasar.

Bayanan ministan na kunshe ne cikin jawabin da ya gabatar yayin taron masu ruwa da tsaki kan harkar sufurin jiragen sama karo na 10 da aka kammala a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Tasoshin jiragen saman da abun zai shafa kamar yadda ministan ya fada sun hada da filin jirgin sama na kasa da kasa dake Kano da Legas da Fatakwal da kuma birnin Abuja, wanda za a danka su ga masu saka jari domin ci gaba da kula da su, amma duk da haka tasoshin za su ci gaba da kasancewa mallakin gwamnati.

Ministan ya ce yanzu haka ana ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma kamfanonin da suka nuna bukata kan yarjejeniyar, sannan daga baya a sami amincewar majalissar zartarwa ta kasa kafin  yarjejeniyar ta fara aiki.

Sanata Hadi Sirika ya ci gaba da cewa, shirye-shirye sun kammala na fara aikin kamfanin sufurin jiragen sama na Najeriya wato Air Nigeria zuwa nan da 29 ga watan Mayun wannan shekarar, a wajen daya kuma ana kan tattaunawa da kamfanin jiragen sama na kasar Habasha wanda shi ne za a damkawa hakkin tafiyar da kamfanin na Air Nigeria bisa yarjejeniyar kasuwanci.

Ministan ya ce yanzu haka gwamnati ta cimma kaso 90 cikin 100 na tsare-taren yadda hada-hadar kamfanin na Air Nigeria zai kasance, inda ya yi fatan gwamnati mai zuwa za ta karasa.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da kulawa sosai wajen sake fasalta tsarin harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya, kuma muna da yakinin cewa za mu iya cimma burin mu na ganin cewa, Air Nigeria ya fara aiki kamar yadda aka tsara, a zancen nan da ake yi babu wani filin jirgin sama a kasar nan da ba a yi masa gyara tare da samar masa da kayayyakin aiki na zamani, wasu ma an kammala yayin da wasu kuma ana kan aiki”.

Sanata Hadi Sirika ya yi fatan cewa, duk da kalubalen tsadar man jirgi da ake fuskanta a kasar, amma wannan ba zai kashe gwiwar masu saka jari ba a harkar sufurin jiragen sama wajen fadada sana’ar su domin cigaban kasa da raya tattalin arziki.(Garba Abdullahi Bagwai)