logo

HAUSA

Ministan wajen kasar Sin ya gana da takwararsa ta New Zealand

2023-03-25 16:37:27 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan wajen kasar Qin Gang, ya gana da takwararsa ta New Zealand Nanaia Mahuta dake ziyarar aiki a kasar Sin.

Yayin ganawar tasu a jiya Juma’a, Qin ya ce tun kafuwar dangantakar diflomasiyyar sassan 2, Sin da New Zealand ke nacewa martaba juna, tare da daukar kan su daidai da juna, suna kuma yin hadin gwiwa domin cimma moriya tare, da neman hanyar daidaito duk da kasancewar bambanci.

Qin ya kara da cewa, a bara Sin da New Zealand suka yi bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya, kuma shugabannin sassan 2 sun gana domin cimma matsaya mai muhimmanci. Daga nan sai ya yi fatan sassan 2 za su aiwatar da matsayar da suka cimma, su kuma yi aiki tare wajen kara bunkasa cikakkiyar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa.

A nata bangare kuwa, uwargida Mahuta cewa ta yi, New Zealand na nacewa manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, tana kuma burin ganin sassan biyu sun zurfafa cudanya, da musaya tsakanin al’ummunsu, da fadada hadin gwiwa a fannoni daban daban, ta yadda za su kara cimma muhimman nasarori tare. 

Da ta tabo batu kan kyakkyawan jagorancin Sin a fannin dakile matsalar sauyin yanayi, da kare mabanbantan halittu kuwa, Mahuta ta ce kasashen 2 za su iya yin aiki tare, wajen kare zaman lafiya da tsaro a yankin Asiya da tekun fasifik, su kuma zage damtse wajen wanzar da ci gaba, tare da sassauta kalubalen karuwar dumamar yanayi a duniya baki daya. (Saminu Alhassan)