logo

HAUSA

Sojojin Nijar sun kashe mayakan Boko Haram kusan 20 da kama 83 a kan iyaka da Najeriya

2023-03-25 17:24:29 CMG Hausa

A kwanan baya, sojojin Nijar sun kashe mayakan Boko Haram kusan 20 da kama 83 a kan iyaka da Najeriya. Wannan samame kaudawa ta sama da ta kasa na da manufar karya lagon kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulunci a yammacin Afirka ISWAP da ta raba gari da Boko Haram, da kuma ta kafa cibiyarta cikin dajin Matari a Najeriya inda daga nan ne take shirya kai hare-hare cikin birane da barikin sojoji a Nijar.

Daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

 

A cewar mujallar ayyukan sojojin a yankin Diffa dake kudu maso gabashin Nijar, wannan luguden wuta na da manufar karya lagon kungiyar ISWAP da dakile hanyoyin kai musu abinci da makamai.

Bisa ga wani rahoton da rundunar sojojin Nijar ta bayar, kusan ’yan ta’adda ashirin aka kashe da kama mayakan Boko Haram 83 da aka mika su ga hukumomin Najeriya tare da lalata sansanonin ’yan ta’adda uku, da kayayyaki da babura da sanya hannu kan makamai da dama.

Sojojin Nijar na rundunar hadin gwiwa FMM da ke kunshe da sojoji 8500 na kasashen Nijar, Nijeriya, Chadi da Kamaru, an kafa ta a shekarar 2015, domin yaki da kungiyoyi masu kaifin kishin addini, suka kai wannan samame daga ranar 13 zuwa 19 ga watan Maris.

A daya gefe, sojojin Nijar sun bayyana cewa sun mika mutane 1121 da ake zargi da mayakan Boko Haram, daga cikinsu akwai mata da yara ga hukumomin Najeriya.

Mutanen suna rayuwa a dajin Sambisa dake arewa maso gabashin Najeriya, suna kokarin shiga tsibiran Nijar na tafkin Chadi domin gujewa yake-yake tare da kungiyar ISWAP.

A cewar rundunar sojojin Nijar, fadan da ake gabzawa tsakanin ISWAP da Boko Haram tun yau da ’yan watanni ya tilastawa iyalai da dama ficewa daga dajin Sambisa domin neman mafaka a tsibiran tafkin Chadi na bangaren Nijar.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar