logo

HAUSA

Ministan wajen Sin ya bukaci dunkuelwar duniya mai inganci a taron G20

2023-03-24 09:41:33 CMG HAUSA

 

masu kallo barkanku da war haka, yau za mu je kasar India, mu duba yadda ake gudanar da wani taron kungiyar G20 a can.

 

Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya yi kira da a yi kokarin sa kaimi ga bunkasuwar dunkulewar duniya baki daya, da karfafa hadin gwiwar bangarori daban-daban a yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da ake yi a New Delhin kasar Indiya

 

Yayin da yake gabatar da jawabin karfafa hadin gwiwar bangarori daban-daban da inganta ci gaban duniya a yayin taron Alhamis din nan, Qin ya bukaci manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, da su dauki nauyin yin aiki tare domin ci gaban duniya da samun wadata.