logo

HAUSA

Najeriya ta bukaci kasashen dake yankin tafkin Chadi da su yi kokarin dakile yaduwar kananan makamai

2023-03-24 11:20:00 CMG HAUSA

 

A ranar Alhamis 23 ga wata a birnin Abuja yayin taron masu ruwa da tsaki na yankin tafkin Chadi, gwamnatin Najeriya ta yi kira ga kasashen dake yankin da su samar da wata kafar sadarwa ta hadin gwiwa da za ta warware matsalolin yaduwar kananan makamai a yankin.

Sakataren gwamnatin Najeriya Mr. Boss Mustapha ne ya yi kiran a jawabin da ya gabatar yayin taron na tsawon yini biyu da za a kammala a yau Jumma’a

Taron mai taken fafutukar dakile yaduwar kananan makamai a yankin tafkin Chadi, cibiyar yaki da yaduwar irin wadanan mamakai tare da hadin gwiwa da ofishin mashawarcin shugaban Najeriya kan al’amuran tsaro ne suka dauki ragamar shirya shi, wanda kuma ya samu halartar wakilan kasashen uku dake yankin tafkin Chadi wadanda suka hadar da Nijar, da Kamaru da Chadi.

Sakataren gwamnatin tarayyar ya ce kamata ya yi Najeriya da sauran kasashen yankin tafkin Chadi su yi amfani da wannan taro domin kawo karshen yaduwar makamai a yankin.

Ya ci gaba da cewa yawaitar makamai a tafkin Chadi babbar matsala ce ga yanayin tsaro a yankin, domin kuwa ya taimaka wajen kara haifar da tashe-tashen hankula a yankunan lamari da ya kasance kuma silar koma bayan tattalin arzikin kasashen dake yankin.

Sakataren gwamnatin tarayyar ya kuma jaddada bukatar aiki tare don aiwatar da yarjejeniyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya da ake da su kan sarrafa kananan makamai da kuma inganta aiwatar da sabbin batutuwa.

A nasa jawabin mashawarcin shugaban Najeriya kan al’amuran tsaro Major Janaral Babagana Mongonu mai ritaya cewa ya yi irin illar da yaduwar kananan makamai ke haifarwa ci gaban rayuwar al’umma ba za su taba misaltuwa ba.

Dole mu kasashen dake wannan yanki mu hada kanmu domin magance matsalolin da suka addabe mu a wannan shiyya musamman batun talauci, koma bayan ci gaba kana da rashin shugabanci na-gari.

Major janaral Babagana Munguno ya kara da cewa saboda damuwar da Najeriya ke da shi kan wannan al’amari ya sa ta samar da cibiya ta musamman da take kula da matsalolin yaduwar kananan makamai a Najeriya.

Ya ce matsalar yaduwar kananan makamai ba abu ne da za a dauke shi da wasa ba, wajibi ne a sami hadin gwiwa mai karfi da nufin samar da mafita cikin hanzari. (Garba Abdullahi Bagwai)