logo

HAUSA

Xi: Ya dace a tabbatar da ingancin ci gaban tattalin arziki bangarori masu zaman kansu

2023-03-24 10:03:33 CMG HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wasu mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, a ranar Litinin da ta gabata, inda ya yi tsokaci kan dabarar raya bangarorin tattalin arziki masu zaman kansu. Bari mu duba yadda aka gudanar da taron.#

 

Shugaba Xi ya kara karfafa wa kamfanoni masu zaman kansu gwiwa da su kara kokari domin cimma burin tabbatar da ingancin ci gaban tattalin arziki bangarori masu zaman kansu.

 

Shugaban ya  jaddada cewa, kasar Sin tana nacewa kan manufar raya tattalin arziki mallakar gwamnatin kasa, tare kuma da raya tattalin arzikin bangarori masu zaman kansu.

 

Xi ya kara da cewa, ya dace kamfanoni masu zaman kansu su kara fahimtar sabon tunanin raya tattalin arziki, ta yadda za su cimma burin tabbatar da ci gaba mai inganci. Kuma ya karfafa wa 'yan kasuwan kasar gwiwar zuba jari kan manyan ayyukan kasa, domin sauke nauyin dake wuyansu na ingiza wadatar daukacin al'ummar Sinawa. (Jamila)