logo

HAUSA

Bazara tana zuwa

2023-03-24 10:02:03 CRI

 Abokai masu kallonmu, yau za mu kewaya filayen gonaki, don mu duba yadda yanayin bazara yake.

Yanzu an kama hanyar shiga lokacin bazara, yawan zafi yana karuwa, an fara gudanar da aikin gona a wasu sassan kasar Sin, inda manoma suke fama da ayyuka iri daba daban, alal misali, gyara gonaki, shuka ire-iren hatsi, dasa ‘ya’yan itatuwa, fesa takin zamani da jiragen sama masu sarrafa kansu da sauransu, al’ummar Sinawa masu himma da kwazo suna yin kokari a yanayin bazara domin gina makomarsu mai kyau.