logo

HAUSA

Irin shinkafa mai inganci na Sin zai kawo girbin hatsi mai yawa ga Najeriya

2023-03-24 09:47:53 CRI

Masu kallonmu, barka da war haka! Kamar yadda kuka sani, aikin gona shi ne tushen tattalin arzikin ko wace kasa, a cikin shirinmu na yau, za mu duba yadda ake gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da tarayyar Najeriya a bangaren aikin gona.

Manoman tarayyar Najeriya suna fama da matsaloli daban daban wadanda suka hada da aikin gona da irin shinkafa maras inganci, da sauyin yanayi, da tsadar takin zamani da sauransu, amma yanzu sun nuna sha’awa kan irin shinkafa mai inganci na kasar Sin.

Masanan kimiyyar aikin gona na kasar Sin da gwamnatin kasar Sin ta tura zuwa yankin arewa maso tsakiyar Najeriya suna gudanar da aikin shuka irin shinkafa mai inganci ba tare da gurbata muhalli ba, inda suke gwajin ire-iren shinkafa da yawansu suka kai 79, wadanda suke iya jure tasirin sauyin yanayi yayin da suke girma.

Masanan da abin ya shafa sun bayyana cewa, da alamun sabbin ire-iren shinkafa za su taka rawa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda Nuhu Danle Ma’an ya yi tsokaci cewa, manoma za su samu karin hatsi sakamakon amfani da sabbin irin, a sanadin haka, al’ummun kasar za su samu karin kudin shiga da guraben aikin yi, yayin da gwamnatin kasar za ta samu karin haraji.