logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a soke yarjejeniyar AUKUS

2023-03-24 10:49:47 CMG HAUSA

 

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga wasu kasashe da su janye shawarar da suka yanke kan hadin gwiwar jirgin karkashin teku mai amfani da makamashin nukiliya.

Geng Shuang ya bayyana cewa, yana da matukar muhimmanci a wannan lokaci, a tabbatar da aiwatar da dokokin hana yaduwar makaman kare dangi yadda ya kamata

Geng ya shaidawa kwamitin sulhun MDD cewa, ba tare da la'akari da tambayoyin da aka gabatar da ma adawa da aka nuna ba, wasu kasashe sun kudiri aniyyar ci gaba da yin hadin gwiwa kan jirgin karkashin teku mai amfani da makamashin nukiliya, ta hanyar fakewa da abin da aka kira kawancen tsaro na kasashe uku. Kasashe biyu da suka mallaki makamin nukiliya da kuma kasashe masu neman yin watsi da yerjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, ba zato ba tsammani, sun shirya tura tan-tan na sinadaran uranium da aka tace, zuwa wata kasa da ba ta da makaman nukiliya.

Geng yana magana ne kan wani shiri na hadin gwiwa, kan hadin gwiwar jirgin karkashin teku mai amfani da makamin nukiliya tsakanin Australiya da Amurka da Birtaniya, wanda aka fi sani da AUKUS. (Ibrahim Yaya)