Kugiza: Demokuradiyyar kasar Sin na kara samun ci gaba
2023-03-24 15:54:37 CMG Hausa

Daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Maris, an gudanar da taron kasa da kasa karo na biyu kan "Dimokuradiyya: Muhimman darajoji ga daukacin bil-Adama" a nan birnin Beijing, fadar mukin kasar Sin.
A yayin taron, mamban hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar Uganda Kugiza Kaheru, ya shaidawa manema labarai cewa, daukacin tsarin demokuradiyyar kasar Sin ya samo asali ne daga tushen tarihin al'adu, kuma jigonsa shi ne ci gaba da koyo, da ci gaba da koyi daga sauran sassa, da ci gaba da daidaitawa, da raya kasa, da kuma samun bunkasuwa bisa sauyi da zamani. Demokuradiyyar kasar Sin ba ta da tsauri da ra'ayin mazan jiya, amma tana da kyau wajen daidaita bukatun al'umma. Ba kawai a ka'idance ba ce, amma a aikace. (Ibrahim)
