logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun ceto mutane a kalla 201 da aka yi garkuwa da su a cikin makonni biyu da suka gabata

2023-03-24 13:57:43 CMG HAUSA

 

Jiya ne, ma'aikatar tsaron Najeriya ta sanar da cewa, a cikin makonni biyu da suka gabata, sojojin kasar sun yi nasarar kubutar da mutane 201 da aka yi garkuwa da su, a yayin wasu hare-haren da sojoji suka kai a jihohin Borno da Kaduna da ke arewacin kasar.

Bugu da kari, jimillar 'yan ta'addan Boko Haram ko reshen Afirka ta yamma na IS da iyalansu 1,506, sun mika wuya ga sojojin Najeriya a wurare daban-daban. (Amina Xu)