logo

HAUSA

Masanin Najeriya: Demokuradiyyar dake damawa da jama’a wata nasara ce da jama'ar kasar Sin suka samu

2023-03-24 10:56:03 CMG HAUSA

 

Daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Maris, an gudanar da taron kasa da kasa karo na biyu kan "Demokuradiyya: Darajoji masu muhimmanci ga daukacin bil-Adama " a nan birnin Beijing.

Darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya, Charles Onunaiju ya shaidawa manema labarai a wurin taron cewa, cikakken tsarin dimokuradiyya da yake damawa da dukkan jama'a a kasar Sin, wata babbar nasara ce da jama'ar kasar Sin baki daya suka cimma karkashin jagorancin JKS. Demokuradiyya ce da ke mai da hankali kan jin dadin jama'a, da nufin ci gaba da inganta yanayin rayuwarsu.

Charles Onunaiju ya ce, a Afirka, muna mai da hankali sosai kan tsarin demokuradiyya da mulkin demokradiyya wanda ke jaddada dokoki, amma ba a mayar da hankali wajen taimaka wa mutane tunkarar kalubalen rayuwa. "Ina fatan dukkan kasashe, musamman kasashe masu tasowa na Afirka, za su nazarci cikakken tsarin demokuradiyyar jama'ar kasar Sin da ya kunshi jama’a a dukkan matakai, kuma su fahimci cewa, demokuradiyya ba wai kawai ta kunshi ka'idojin aiki ba ne, har ma da bukatar biyan hakikanin bukatun jama'a." (Ibrahim Yaya)