logo

HAUSA

Majalissar zartaswar gwamnatin Najeriya ta amince da kashe tsabar kudi har Naira biliyan 459 don kammala wasu ayyuka

2023-03-23 14:21:32 CMG Hausa

A ranar Laraba 22 ga wata, majalissar zartaswa ta tarayyar Najeriya ta amince da kashe kudi har Naira biliyan 459 domin kammala wasu ayyuka a ma’aikatar sufurin kasar tare kuma da gina rukunin gidajen ma’aikatan hukumar yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi na kasar.

Majalissar ta amince da wannan kudiri ne yayin taronta na mako-mako wanda ta saba gudanarwa a duk ranar Laraba karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.