logo

HAUSA

Shugaban kasar Nijar na son ciyar da kwallon kafar kasarsa gaba

2023-03-23 21:01:21 CMG Hausa

A kwanan baya, shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya jagoranci wani zaman taro na manyan jami ai kan zuba a fannin wasannin motsa jiki musammun ma game da wasan kwallon kafa a fadar shugaban kasa dake birnin Yamai, ganin yadda kasar Nijar take kokarin kama hanya a bangaren wasan tama’ula da ma sauran wasannin motsa jiki a dandalin kasa da kasa.

Haduwar dai ta samu halartar faraminista Ouhoumoudou Mahamadou, ministan kudi da ministan matasa da wasannin motsa jiki da kuma shugabannin kungiyar kwallon kafa ta kasa cewa da FENIFOOT. Wannan zaman taro da irinsa ne na farko na da manufar shata tsarin zuba kudi mai karko cikin wasannin motsa jiki, musamman ma a bangaren kwallon kafa da kuma kafa yanayi mai kyau domin yin gogayya da sauran kasashen duniya ta fuskar wasan kwallon kafa, a cewar mai bada shawara na ma’aikatar matasa da wasannin motsa jiki, Alhaji Tiemago Ibrahim, tare da tunatar da cewa shugaban kasa har kullum na kawo goyon bayansa ga wasannin motsa jiki na kasa. Anan shi ne na kawo matasan Nijar da suke da kwarewa da gwaninta da nuna kansu a cikin gasannin kasa da kasa domin daukaka tutar kasar Nijar a idon duniya.

Wasan motsa jiki na Nijar, tare da rakiyar shugaban kasa Mohamed Bazoum, na nan na samun tagomashi kuma wannan tattauanwa tare da masu ruwa da tsaki a fannin kwallon kafa da ma sauran wasannin motsa jiki za ta kara taimakawa wajen sanya kasar Nijar a hannun gaban kasashen duniya musammun ma a nahiyar Afirka kenan domin haka ne ya nada kyau hukumomin kasa su mai da hankali sosai in ji Alhaji Tiemago Ibrahim.


An binne gawar dan kwallon kasar Ghana da ya rasu sakamakon girgizar kasa a Turkiyya


Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya jagoranci jami’an gwamnatin sa zuwa inda aka ajiye gawar dan wasan kwallon kafar kasar Christian Atsu, a ranar Juma’ar karshen makon jiya, domin halartar jana’iza, da bayyana alhinin su ga rasuwar dan wasan, gabanin binne shi.

Dan wasan dake bugawa kungiyar Black Stars ta Ghana kwallo, yana taka leda a Turkiyya ne lokacin da girgizar kasa ta aukawa wasu biranen kasar, ta kuma yi sanadin rasuwar sa cikin watan da ya gabata.

Baya ga shugaban na Ghana, sauran manyan jami’an gwamnatin kasar da suka halarci jana’izar dan kwallon su ne mataimakin shugaban kasa Mahamudu Bawumia, da tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama, da iyalai da jami’an jakadancin kasar Turkiyya dake Ghana, da tsofaffin ‘yan kwallon kasar, da sauran abokan arziki, wadanda dukkanin su ke cike da bakin cikin rasuwar dan wasa.

Cikin takardar jajantawa da ministan ma’aikatar matasa da wasanni Mustapha Ussif ya karanta a madadin gwamnatin kasar, gwamnatin Ghana ta ce al’ummun kasar za su jima suna tunawa da tsohon dan wasan bisa kwazon sa da jajircewa.

Takardar ta ce "Gwamnati da daukacin al’ummar Ghana, za su ci gaba da tunawa da Christian Atsu, a matsayin daya daga ‘yan wasa mafiya hazaka, da kwazo kuma masu son cimma nasarori, wadanda suka yi fice a kwallon kafar wannan lokaci".

An gano gawar Atsu ne bayan kwanaki 12 da aukuwar girgizar kasar da ta girgiza Türkiyya da wani bangare na Syria. Kafin hakan, dan wasan mai shekaru 31, ya bace lokacin da gine-gine suka rushe sakamakon girgizar kasar da safiyar ranar 6 da watan Fabarairu.


Wani koci a Namibia yana kokarin ingiza sana’ar wasanni ta masu bukatar musamman


Richard Goreseb, mai horas da ‘yan wasa ne a kasar Namibia, wanda a yanzu haka yake kokarin ganin ya horas da karin masu bukatar musamman a fannonin wasannin motsa jiki, ta yadda za su kai ga shiga manyan wasannin kasa da kasa.

Richard Goreseb, wanda ke zaune a birnin Windhoek fadar mulkin kasar, ya jima yana horas da ‘yan wasan motsa jiki tun daga matakin farko, ya kuma lura cewa, ‘yan wasa masu larurar gabbai na fuskantar kalubale da nuna banbanci, kana ba sa samun masu karfafa musu gwiwa sosai. Don haka bayan ya kammala halartar gasannin motsa jiki a farkon shekarar 2016, sai ya yi ritaya tare da mayar da hankali ga karfafa gwiwar sauran ‘yan wasa dake ajin masu bukatar musamman.

A cewar Richard Goreseb "Ina fatan karfafa gwiwar wasu, da horas da wasu, tare da gina kwazon wadanda aka bari a baya".

Horon da yake bayarwa na maida hankali ne kan gudummawar dukkanin sassan gina kwazon wasannin motsa jiki, da samun gogewa wajen sarrafa jiki da sauri, da gano wasa mafi dacewa da dukkanin masu fara wasannin, da ma wadanda suka manyanta.

Ayyukan suna da yawa. A cewar Goreseb, Abu ne mai muhimmanci a taimaka musu, ta yadda za su kawar da duk wani shinge na tunani da na zahiri, har su kai ga bude sabon babi a rayuwar su, wanda zai taimaka musu a gabar da suke fuskantar kalubale daga sauran sassan al’umma.

Ya ce "Dole na rika hangen nesa, sama da batun larurar gabbai da suke da ita, ta yadda zan zakulo damar ko wane dayan su, ta kawar da shingen tunani dake hana shi ci gaba. Na koyi horas da ‘yan wasa ta hanyar halartar kwasa-kwasai a nan Namibia".

Goreseb mai shekaru 46 a duniya, yana kuma aiki tare da wata kungiyar wasannin motsa jiki dake Namibia mai suna “Lions Sports Club”, wadda karkashin ta masu horas da ‘yan wasa da dama ke hadin gwiwar renon ‘yan wasa ajin masu cikakkiyar lafiya, da ma masu bukatar musamman, ta yadda dukkanin su za su cimma cikakkiyar moriya.

Tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu, kocin ya horas da sama da ‘yan wasa 150, mafiya yawan su kuma sun cimma manyan nasarori, ta yadda hakan ya daga matsayin wasannin motsa jiki ajin masu bukatar musamman a matsayin gasannin kasa, da na kasa da kasa.

Yayin da ya halarci aikin horaswa a matsayin kasa da kasa karon farko, Goreseb ya jagoranci tawagar ‘yan wasan motsa jiki zuwa wasanni da suka baiwa kasar damar lashe lambobin yabo 17. Ya horas da manyan ‘yan wasan motsa jiki ajin masu bukatar musamman ciki har da Johannes Nambala, wanda ya fafata a gasar tseren T13.

Kaza lika a baya bayan nan, ya horas da dan wasan tseren keke Nico Kharxab, wanda kuma hakan ya baiwa dan wasan damar shiga a dama da shi a gasar da hukumar wasanni ta Afirka ta kudu, ajin masu bukata ta musamman ta shirya a makon jiya a birnin Cape Town.

Da yake tsokaci game da hakan, Kharxab ya ce wannan horo da ya samu daga koci Goreseb, ya karfafa masa damar shiga gasanni, har da na kasa da kasa, tare da samun karfin gwiwar cimma nasarori.

Kharxab ya ce "Masu horaswar sun samar mana da damar kara kwarewa, wanda hakan ya ba mu damar shiga a dama da mu cikin gasanni cikin karfin gwiwa, musamman lokacin da muke tunkarar abokan fafatawa, ta yadda ba za mu ja da baya ba duk wahala".

Duk da nasarorin da ake samu, wasu kalubalen na ci gaba da wanzuwa. Da yawa daga ‘yan wasan motsa jiki na shan fama da matsaloli yayin da suke neman samun horo, sakamakon rashin kudaden sufuri, wasu kuwa na yin horon alhali suna fama da yunwa, don haka wasun su kan yi watsi da horon. Goreseb yana sane cewa, da dama suna sha’awar wasanni, kuma wasu lokutan yana taimaka musu daga cikin albashin sa. Ya ce "Ina fatan ganin Namibia ta zama gidan kwararrun ‘yan wasa".

Michael Hamukwaya, babban sakataren kwamitin shirya wasanni ajin masu bukata ta musamman a Namibia, ya ce aikin masu horas da ‘yan wasa ya wuce batun samar da kwarewa, domin kuwa, suna ma wayar da kan al’ummu tare da fadakarwa.

Hamukwaya ya ce "Burin mu shi ne kawar da duk wani nau’i na nuna wariya domin rungumar kowa da kowa".