Ziyarar sada zumunta da hadin gwiwa da kokarin kawo zaman lafiya
2023-03-23 21:32:41 CMG Hausa
A wannan makon ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki kasar Rasha daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Maris. Wannan ita ce ziyara ta farko da Xi Jinping ya kai zuwa ketare, tun bayan da aka sake zabarsa a matsayin shugaban kasar, kuma ziyara ce ta sada zumunci da tabbatar da hadin gwiwa da zaman lafiya, da karfafa dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani.
Duk wani irin ci gaba da aka samu, kan dangantakar Sin da Rasha, ba za ta rasa nasaba da jagorancin shugabannin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare ba. Sin da Rasha sun yi nasarar shimfida hanyar amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare a tsakanin manyan kasashen duniya, da yin mu'amalar sada zumunta tsakanin kasashen da ke makwabtaka, lamarin da ya zama abin koyi ga karfafa huldar kasa da kasa.
A yayin wannan ziyara, shugabannin biyu sun yi tattaunawa kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu, da manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da suka shafi moriyar juna, sun kuma cimma sabbin fahimtar juna masu muhimmanci a fannoni da dama.
Shugabannin biyu sun kuma rattaba hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa ta jamhuriyar jama'ar kasar Sin da tarayyar Rasha, kan zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani da kuma sanarwar hadin gwiwa na shugaban kasar Sin da na shugaban Tarayyar Rasha, kan shirin raya kasa nan da shekarar 2030 kan abubuwan da suka sanya a gaba a hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen Sin da Rasha.