logo

HAUSA

FAO ta samu dalar Amurka miliyan 27 don bunkasa ayyukan jin kai a gabashin Afirka

2023-03-23 10:57:13 CMG Hausa

Hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD (FAO), ta yi maraba da dalar Amurka miliyan 26.9, da ta samu, don samar da abinci da sauran kayayyaki da ayyukan yau da kullun a gabashin Afirka.

Hukumar FAO ta bayyana cewa, za a yi amfani da kudaden da aka samu daga kasar Jamus ne, wajen karewa da kuma sake farfado da ababen more rayuwa a yankunan da fari ya shafa, a kasashen Habasha, Kenya, Somaliya da kuma Sudan.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta bayyana cewa, sabon tallafin wata babbar gudummawa ce, a kokarin da ake yi na dakile illolin fari, kan samar da abinci da harkoki na rayuwa, ta hanyar kara kai agajin gaggawa a yankunan karkara, da kiyayewa da dawo da al’amuran rayuwa, da ba da damar dogaro da kai cikin sauri.

Ta ce, tallafin na fatan kaiwa ga kusan mutane miliyan 1 daga cikin mutanen da suka fi rauni a yankunan karkara, kuma ake da wahalar isa gare su, a dukkan harkoki na rayuwa.

A cewar FAO, daga cikin wadannan kudade, kasar Habasha za ta samu dala miliyan 7.54, Kenya dala miliyan 7, Somaliya za ta samu tallafin dala miliyan 8.08, yayin da Sudan za ta samu dalar Amurka miliyan 4.31. (Ibrahim Yaya)