logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Rasha na da muhimmanci sosai ga duniya

2023-03-23 10:22:36 CMG Hausa

A jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kammala ziyarar aiki a kasar Rasha, tare da cimma dimbin sakamako, wanda ya nuna cewa ziyararsa a wannan karo tana da ma’anar tarihi, wadda ta tabbatar da zumunci da hadin kai, gami da zaman lafiya.

Ziyarar shugaba Xi ta nuna a zahiri cewa, kasar Sin na martaba manufar diplomasiya mai zaman kanta. Kana kasar ta tsai da kudurin karfafa huldarta da kasar Rasha ne, bisa la’akari da moriyarta, da yanayin ci gaban harkokin siyasa na duniya, saboda haka ba za ta canza wannan manufa bisa abkuwar wani lamari ba.

Haka zalika, yayin ziyararsa a kasar Rasha, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, sun sa hannu kan hadaddiyar sanarwar zurfafa huldar abota tsakanin Sin da Rasha, bisa manyan tsare-tsare. Wannan sanarwar ta nuna ra’ayi na bai daya da kasashen 2 ke da shi, kan dimbin al’amuran kasa da kasa.

Ban da haka kuma, wannan sanarwar ta kunshi bayanai masu alaka da batun kasar Ukraine, inda bangarorin Sin da Rasha suka jaddada cewa, sauke nauyi da kuma gudanar da shawarwari, su ne hanyoyi mafi dacewa na daidaita rikicin Ukraine.

Bisa la’akari da nagartaccen sakamakon da aka samu a ziyarar da shugaba Xi ya kai kasar Rasha, muna iya cewa, hadin gwiwar kasashen Sin da Rasha na taimakawa wajen tabbatar da dimokuradiya a huldar kasa da kasa, da samar da tabbaci ga kasashe daban daban, ta hanyar tallafawa kokarinsu na neman tsaro da ci gaban al’umma. (Bello Wang)