logo

HAUSA

Firaministan Sin ya jaddada bukatar bunkasa masana'antu

2023-03-23 10:51:33 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira da a kara ba da fifiko, wajen samun bunkasuwa mai inganci, da mai da hankali kan ci gaban masana’antun samar da kayayyaki da hidima, da raya fasahar kirkire-kirkire da karfin masana’antu na yin takara, da kokarin bunkasuwar masana'antu, da hanzarta aiwatar da ayyuka masu inganci, da gina tsarin masana'antu na zamani.

A yayin ziyarar da ya kai wasu masana'antu dake Zhuzhou da suka hada da kamfanin kera jiragen kasa na CRRC Zhuzhou Locomotive Co., Ltd., firaministan ya ganewa idonsa dalla-dalla kan yadda ake samarwa, bincike da ci gaba, da bunkasuwar kasuwannin kamfanonin.

Ya ce, inganta ci gaban masana'antu, ya dogara ne a kan kirkire-kirkire da kuma basira. Don haka, ya dace kamfanoni su hanzarta cimma nasarori, a manyan fasahohi da kayan aiki.

Li ya bayyana cewa, kima da kuzarin kirkire-kirkire na fasaha, ya dogara da yadda ake amfani da shi.  Don haka, ya bukaci karin hadin kai tsakanin masana'antu, da masana, bincike da aiwatarwa, kana ya yi kira da a kara daga matsayi da ingancin kayayyaki.

Yayin ziyarar da ya kai a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan kuwa, Li ya bayyana cewa, masana'antu su ne babban bangaren kirkire-kirkire, don haka ya kamata a yi kokarin raya masana'antun da babu kamar su a duniya da wadanda ke amfani da fasahohi na musamman na zamani, wajen samar da sabbin kayayyaki da na musamman. (Ibrahim Yaya)