logo

HAUSA

An gudanar da zaman tattaunawar kafofin watsa labaran Sin da Rasha mai taken "zamanantarwa iri ta kasar Sin da sabbin damammaki na duniya"

2023-03-22 20:49:19 CMG Hausa

A yau Laraba 22 ga wata ne aka gudanar da zaman tattaunawa na kafofin watsa labaru na Sin da Rasha mai taken "zamanantarwa iri ta kasar Sin da sabbin damammaki na duniya", wanda babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, da rukunin kafofin watsa labaru na kasa da kasa na Rossiya Segodnya suka shirya tare, a kwalejin huldar kasa da kasa ta Moscow.

Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban CMG, Shen Haixiong, tare da jami’an manyan cibiyoyin watsa labaru da na jami'o'in kasar Rasha, da jami'an gwamnati, da kwararru, da masana na Sin da Rasha da dai sauransu sun halarci zaman. Sun kuma tattauna tare da yin musayar ra’ayi sosai kan batun "Hanyar Zamanantarwa Mai Dacewa da Halin Kasa".

Kaza lika mahalarta taron baki daya suka amince da cewa, kasar Sin ta hau tafarkin zamanantar da kanta bisa yanayin da take ciki, wanda ya samar da kyakkyawan misali ga sauran kasashe, tare da bude wata sabuwar hanya ta wayewar kan dan Adam. (Mai fassara: Bilkisu Xin)