logo

HAUSA

CMG ya rattaba hannu kan takardar tunatarwar hadin gwiwa da jaridar Rasha

2023-03-22 09:58:42 CMG Hausa

A yayin ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping ya kai kasar Rasha, mataimakin ministan yada labarai na kwamitin kolin jam‘iyyar kwaminis ta kasar Sin Shen Haixiong, shugaba kuma babban editan gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, da darekta Negoitsa na jaridar kasar Rasha, Rossiyskaya Gazeta, jarida mafi girma a Rasha, sun sanya hannu kan “takardar tunatarwar hadin gwiwa tsakanin babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da jaridar kasar Rasha”. (Ibrahim)