logo

HAUSA

Xi ya gana da Putin a Moscow

2023-03-21 09:40:25 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, a fadar Kremlin a lokacin da ya isa birnin Moscow jiya Litinin.

Xi ya jaddada cewa, akwai kyakkyawar fahimta ta tarihi a dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha kafin ta kai inda take a yau. Kasashen Sin da Rasha manyan makwabtan juna ne, kuma abokan hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. Haka kuma kasashen biyu na kallon dangantakarsu a matsayin wani babban fifiko a fannin diflomasiyya da manufofinsu kan harkokin waje.

Har kullum kasar Sin tana kiyaye manufofin ketare mai cin gashin kai. Xi ya ce, karfafa dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha, wani muhimmin zabi ne da kasar Sin ta yi bisa manyan muradunta da kuma yanayin da duniya ke ciki.

Shugaba Xi ya ce, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kiyaye da karfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da kasar Rasha. Yana mai cewa, Sin da Rasha sun kuduri aniyar tabbatar da ci gaba da sake farfado da kasashensu, da nuna adawa ga masu amfani da nuna karfin tuwo a duniya, da kokarin tabbatar da tsarin demokuradiyya mai inganci a alakar kasa da kasa.

Xi ya ce, ya kamata kasashen biyu su kara zurfafa hadin gwiwa a aikace a fannoni daban-daban, da karfafa hadin gwiwa a hukumomin kasa da kasa kamar MDD, don bunkasa ci gaban kasa da sake farfado da su, da kuma zama tushen zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

A nasa jawabin shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta samu nasarori masu ban sha'awa da ma manyan nasarori a dukkan fannonin ci gaba. Wannan a cewarsa, na da nasaba da kyakkyawan shugabanci na Xi, kuma ya tabbatar da karfin tsarin siyasa da tsarin mulki na kasar Sin.

Putin ya ce, yana da kwarin gwiwar cewa, karkashin jagorancin shugaba Xi, ko shakka babu kasar Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa da nasarar cimma dukkan manyan manufofin da aka sanya a gaba. Haka kuma, shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayi mai zurfi kan batun Ukraine. (Ibrahim Yaya)