logo

HAUSA

Sin ta soki Amurka da nuna fuska biyu kan batun zirin Koriya

2023-03-21 12:45:24 CMG HAUSA

 

Jiya Litinin, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taro kan halin da ake ciki a zirin Koriya. Yayin taron, wakilin Sin ya yi Allah wadai da kalaman Amurka da ma matakin fuska biyu da take nunawa kan batun.

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang ya nuna cewa, kamata ya yi mambobin kwamitin su yi kokarin karawa Koriya ta Arewa kwarin gwiwar maido da shawarwari, ta yadda za a shimfida sharadi mai kyau da sassauta halin da ake ciki a zirin.

Geng Shuang, ya kuma ya yi tir da fuska biyu da Amurka ke dauka, wato a bangare daya ta sanyawa Koriya ta Arewa takunkumi, a bangare daya kuman ta sayarwa Austriliya kayayyakin nukiliya da za iya hada makamai da su. Ya kuma yi kira ga daidaikun kasashe, da su saurari kiran da al’ummar duniya da na shiyya-shiyya ke yi, sun yi watsi da tunanin yakin cacar baki da siyasar kungiya, ta neman biyan bukatunta da na kewayenta da dakatar da magudin siyasanta, da cika alkawuran da ya rataya a wuyansu na hana yaduwar makaman nukiliya, da yin watsi da kudurin da suka tsai da shi na hadin kai a bangaren kira jirgi karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, da ma daukar matakan da suka dace don warware batun zirin a siyasance. (Amina Xu)