logo

HAUSA

MDD: A kalla mutane dubu 43 ne suka mutu a Somaliya sakamakon fari a shekarar 2022

2023-03-21 09:57:10 CMG HAUSA

 

Hukumomin MDD biyu da kasar Somaliya sun bayyana cewa, an yi kiyasin mutane fiye da dubu 43 ne suka mutu a shekarar 2022, sakamakon tsananin fari, adadin da ya zarta na shekarar farko na farin da ya afkawa kasar a shekarar 2017 zuwa 2018.

Hukumar lafiya ta duniya WHO, da asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF), da ma'aikatar lafiya da ayyukan jin kai ta Somalia, sun bayyana a cikin wani rahoton hadin gwiwa da aka fitar a Mogadishu, babban birnin kasar cewa, rabin adadin mace-macen da aka samu sanadiyar fari, ya shafi yara ne 'yan kasa da shekaru biyar.

Ministan kiwon lafiya na kasar Somaliya Ali Haji Adam Abubakar, ya bayyana damuwa game da matsayi da ma girman tasirin matsalar karancin abinci da ke kara tsananta a kasar.

A cewar rahoton, an yi hasashen adadin mace-macen zai kai kaso 0.42 a cikin mutane dubu 10 a kowace rana nan da watan Yunin shekarar 2023.

Wakilin WHO Mamunur Rahman Malik ya ce, suna fadi tashin gani, sun magance mace-macen da kuma ceton rayukan wadanda suke da sauran numfashi. (Ibrahim Yaya)