logo

HAUSA

Ministan wajen Equatorial Guinea zai ziyarci kasar Sin

2023-03-21 19:24:39 CMG Hausa

Bisa gayyatar da dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang ya yi masa, ministan harkokin waje, da hadin gwiwar kasa da kasa, da harkokin da suka jibanci ‘yan kasa mazauna ketare na kasar Equatorial Guinea, Mr. Simeon Oyono Esono Angue, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, tsakanin ranekun 22 zuwa 26 ga watan nan na Maris.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin ne ya bayyana hakan a yau Talata.  (Saminu Alhassan)