logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a gaggauta dawo da taimakon kudin da ake baiwa Sudan ba tare da wani sharadi ba

2023-03-21 09:56:36 CMG HAUSA

 

Mukaddashin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing ya bayyana cewa, ya kamata kasashe da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa masu ruwa da tsaki, da su dawo da taimakon tattalin arziki da suke baiwa kasar Sudan ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Da yake jawabi yayin taron da kwamitin sulhun ya kira jiya Litinin, Dai Bing, ya kuma bukaci bangarorin da abin ya shafa, da su yi kokarin dage takunkumin da aka kakabawa kasar.

Dai ya ce, kasar Sin ta samu kwarin gwiwa bisa ra'ayin siyasa da kuma shawarwarin da bangarorin da abin ya shafa ke nunawa a fannin siyasar kasar. Yana mai nuni da cewa, an samu ci gaba a harkokin siyasar kasar

Ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan dukkan bangarori, da su goyi bayan tsarin siyasa na Sudan, karkashin jagorancin kasar, da ci gaba da yin shawarwari da dukkan sassa, ta yadda za a kara fadada fahimtar juna, da samun hanyar bunkasuwa da ta dace da yanayin kasar.

Ya ce, yanzu haka yanayin tattalin arziki da na jin kai a kasar Sudan, abin damuwa. (Ibrahim)