logo

HAUSA

An kusa warware rikicin siyasa a Sudan

2023-03-21 09:41:04 CMG HAUSA

 

Babban wakilin MDD a kasar Sudan Volker Perthes, ya fada a jiya Litinin cewa, yanzu haka ana daf da warware rikicin siyasar kasar, duk kuwa da kalubalen da shirin warware takaddamar ke fuskanta.

Volker Perthes ya shaida wa taron kwamitin sulhu na MDD cewa, "a yau, muna kusa da samun mafita, ko da yake akwai kalubale."

A ranar 5 ga watan Disamban shekarar 2022 ne, shugabannin soja da na farar hula a kasar ta Sudan, suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar siyasa, don kawo karshen rigingimun siyasa tare da kafa gwamnatin rikon kwarya ta tsawon shekaru biyu.

Perthes ya ce, yarjejeniyar ta kasance wani zakaran gwajin dafi, kuma ta bijiro da wani sabon babi a tsarin siyasar kasar, wanda ke da nufin kaiwa ga kafa wani sabon shiri na mika mulki. (Ibrahim Yaya)